Spread the love

‘Yan sanda sun kama mutum hudu barayin babur a Kebbi

‘Yan sandan jihar Kebbi  sun kama wasu mutane hudu da ake zargi barayin Mashin ne da suka addabi hanyar Birnin Kebbi zuwa Jega.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Nafi’u Abubakar ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Jumu’a.

Ya ce a 10 ga junairu ne suka samu labarin wasu kwararrin barayin mashin dauke da bindiga sun tafi karamar hukumar Koko, anan take jam’inmu da yake can ya shirya mutanensa suka tafi wurin in da suka samu nasarar cabke mutum huda a cikin barayin da suka hada da Usman Sani da Bashir Usman sun fito ne daga karamar hukumar Gwandu sai Tukur Muhammad daga Birnin Kebbi na hudun Yahaya Kabiru dan kauyen Hegin Ruma ne a garin Gusau jihar Zamfara dukansu matasa ne ba su kai shekara 30 ba.

Abubakar ya ce barayin sun karba laifinsu, su ne ke kwatar babur a saman hanyar Kebbi zuwa Jega.

Da zaran an kammala bincike za a hannunta su gaban kuliya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *