Spread the love

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule  ya ce akwai abubuwan Boko Haram da kungiyar Darussalam ke gudanarwa a jihar

Sule ya tabbatar da bayyanan ‘yan kungiyar Boko haram a jihar hakan ya sanya suke fuskantar matsalar tsaro a kwanannan.

Gwamna Sule ya bayyanawa manema labarai na fadar shugaban kasa a jumu’ar nan bayan ya gama ganawa da shugaban kasa a fadar.

Gwamnan ya ce ‘yan kungiyar na cikin abubuwan da ke kara ruruta wutar  matsalar tsaro a jihar Nasarawa, an tarwatsa sansaninsu  Toto kafin su sake yin mahada a kan iyakar Nasarawa da Benuwe a can ne suke kai farmaki ga mutane.

Gwamna Sule ya ce wasu abubuwan na Boko haram ‘yan kungiyar Darussalam ne da aka koro a jihar Neja ne ke yin su a Nasarawa, an kashe wasu daga cikinsu an  kama 900 a wani sintirin jami’an tsaro na hadin guiwa da aka yi.

Ya ce an samu bayanin ne ta hannu mutanen da aka kama suka fadi su ‘yan Boko Haram ne, suna da tabbacin matakin da aka dauka zai karya lagonsu hakan ya sa ya zo ya yi wa shugaban kasa bayani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *