Spread the love

 

Daga Muhammad M. Nasir.
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya jinjina ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tallafawa aiyukkan gwamnonin Nijeriya 36 domin a samar da cigaba mai dorewa a kasa.
Gwamnan a kalamansa wajen kaddamar da aiyukkan gidaje 744 da hanyar mota da ya samar wadda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tammbuwal ne babban baƙo da zai bude aiyukkan ya ce da Shugaba Buhari bai agaza wa gwamnoni ba da ba wanda zai yi abin a zo a gani.
Ya ce ko da ya karbi jihar ya samu ana biyarta bashin biliyan 92, bayan nan yanzu sun kashe kudi biliyan 120 a ina suka samu kudin, ta hannun gwamnatin tarayya ne.
“Shugaban kasa ya ba mu bailout mu biya albashi, bayan nan kuma ya koma a duk wata sai ya ba mu biliyan daya domin dai biyan albashin har tsawon wata 18.
“Ya ba mu wasu biliyan 10 mu yi aiki, aiyukkan da jihohi suka yi na gwamnatin tarayya an biya kowane gwamna a Jigawa an bamu biliyan 10.” a cewar Badaru.
Ya ce kudin Paris Clob an ba shi sama da biliyan 40, kai Buhari ya yi rawar gani suna godiya sosai, kamar yadda ya fadi a gaban Tambuwal ya nuna cewa shi shaida ne kan kudin, har shaguɓe ya yi ‘Buhari baban Tambuwal ne baban Badaru ne’.
Da ya juya kan Tambuwal ya gode wa karimcin da ya yi wa mutanen Jigawa na aminta ya zo ya ƙaddamar da aiyukkan cigaba, kuma sun gayyaci Tambuwal ne domin mutumin kirki ne mai son cigaba da ɗorewar zaman lafiyar ƙasar Nijeriya.
Ya ce bai kula da bambancin siyasa ba ne domin su a Jigawa babu ruwansu da siyasar gaba da rashin girmama juna, Tambuwal yana da mutuncin da za a girmama shi.
Sai dai  Gwamna Badaru bai jajantawa Tambuwal da mutanen Sakkwato ba kan gobarar da ta laƙume babbar kasuwar Sakkwato a ranar Talatar data gabata wanda hakan ya sa aka ɗage bukin daga Laraba zuwa Jumu’a.
Managarciya na ganin wannan rashin jajantawar mantuwa ce kawai ta kama Gwamnan ko hankalinsa ne ya shagaltu kan bukin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *