Spread the love
Hukumar rarraba wutar lantarki a Kaduna ta yanke wutar gidan tsohon shugaban ƙasa margayi Shehu Aliyu Shagari saboda bashin naira miliyan 6 da ake biyar gidan.
A ranar 28 ga watan Disamba 2018 tsohon shugaban ya rasu yana da shekara 93.
Manema labarai a ƙasar ta rawaito kakakin kamfanin, Abdulaziz Abdullahi na cewa ba a biyan kuɗin wutar tun bayan mutuwar marigayi Shagari.
Kakakin ya kuma shaida wa jaridar cewa an basu wa’adi ko ɗaga musu ƙafa domin biyan kuɗaɗen da ake bin su kafin a yanke wutar.
Wani jami’in gwamnatin Sokoto wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce babu adalci idan aka ɗaurawa gwamnati laifi kan yanke wutar, a cewar Jaridar.
Wasu mutane na ɗaura laifin yanke wutar ga ɗiyansa manya musamman tsohon ɗan majalisar waƙillan Nijeriya Aminu Shehu Shagari da sauran manyan ‘ya’yansa.
Da yawansu suna da aiki ko kasuwancin da suke yi amma har su yi sakacin barin a yanke masu wuta a gidan da mahaifansu ke zaune.
Wannan sakaci ne suka yi gaskiya ba laifin gwamnatin tarayya ko jiha ba ne domin harkar da suke yi ta isa su kula da gidan ba tare da sa hannun kowa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *