Spread the love
 Jam’iyyar APC ta Jihar Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko,  sun jajantawa ‘yan kasuwa dake babbar kasuwar  jihar Sakkwato da Ibtala’in gobara ya shafa a ranar  Talata data gabata.
Sanata Wamakko ya wakilta tsohon kwamishinan gona Alhaji Umaru Nagwari Tambuwal ya jagoranci ayarin shugaban jam’iyar APC ciki har da shugabanninsu 43.
 Mambobin Majalisar dokoki ta Jihar Sakkwato su 13 na Jam’iyyar APC ƙarƙashin jagorancin Jagoransu a  Majalisar dokokin jiha Honarabul Bello Isah Ambarura suna cikin ayarin.
Hakan ke kara tabbatar da cewa Kakakin majalisar dokokin jiha Honarabul Aminu Manya Achida jagororin jam’iyar APC ba su ɗauke shi ɗan jam’iyarsu ba hakan ya sa suka umarci Ambarura ya jagoranci mambobinsu, tun da shi ya zaɓi gwamna Tambuwal a matsayin jagoransa da zai yi tafiya tare da shi.
 Ka sa ambatar sunan Wamakko tare da aika masa saƙon Tambuwal ne jagoransa  a  wurin gidauniyar ƙaddamar da littafin Dakta Jabir Sani Maihula ya ƙara fitowa fili ya nuna kakakin ba ya tare da APC lokaci ne kawai yake jira ya fitar da sanarwa don ruhinsa kam yana wurin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.
Salon siyasar Honarabul Aminu tana da sha’awa amma da wuyar gaske za ta yi ƙarko tala’akari da yadda yake rawar siyasarsa na halin mai da kowa muzi, da wuyar gaske a duk lamari mai raba ƙafa  cikinsa ya yi nasara, in tsayi tau tsayi, in tafiya tau tafiya, a lokaci ɗaya ba a yin tsaye kuma a yi tafiya duk wanda ya ce zai yi waɗannan a lokaci ɗaya akwai buƙatar kai shi ƙasar Nijar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *