Kusan ‘yan bindiga 600 tare da shugabanninsu a jihar Kaduna suka aminta da ajiye makamansu domin wanzar da zaman lafiya.

Sun ba da sanarwar yanke hukuncin bayan haɗuwarsu da malamin addinin musulunci Shaikh Ahmad Gummi da kwamishinan ‘yan sanda Umar Muri a ƙauyen sabon garin yadi cikin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

‘Yan bindigar da matansu sun zubar da hawaye a lokacin da malamin ke masu wa’azi kan zaman lafiya, sun yi alƙawalin samar da zaman lafiya a Giwa da Zariya da hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Sun yi gargaɗi kada jami’an tsaro su riƙa matsa masu da iyalansu su rika ɓata masu abin da suka mallaka.

Matuƙar aka saɓa yarjejeniyar da aka yi da su ta zaman lafiya za su koma cikin daji.

Shugabansu ya yi magana a bukatar da suke da ita na samar da kayan more rayuwa kamar makaranta da asibiti a dukan ƙauyukkansu.

Gumi ya ba da tallafin dubu 500 da kayan sawa da littafan addini don amfanisu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *