Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kara fadada kwamitin gobarar sabuwar  kasuwa da ya kafa  yawasu ya kai mutum 19 a yanzu.

Gwamnan ya kara mutane shida ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin mataimakin gwamna Manir Dan’iya a yau Laraba.

Mutanen da aka kara su ne babban Sakatare a ma’aikatar cikin gida, babban darakta a hukumar ba da agajin gaggawa ta jiha SEMA, wakili daga ma’aikatar shari’a, da jami’an tsaron farin kaya(DSS) da kungiyoyin sa kai da bana gwamnati ba.

Tambuwal ya baiwa kwamitin wa’adin sati daya ya kawo rahotonsa domin daukar mataki na gaba.

Ana bukatar kwamitin ya gano musabbabin wutar da yawan hasarar da aka yi da abin da yakamata gwamnati ta yi tare da la’akari da halin da kasuwar take ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *