Spread the love
Miyetti Allah ta yi tir da Kashe-Kashen da Ake yiwa ‘ya’yanta a Neja
Daga M. A. Umar, Minna
Kungiyar Miyetti Allah ( MACBAN ) tayi tir da kisan da tayi zargin yan banga a karamar hukumar Mashegu da yiwa ‘yayanta.
Mataimakin shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Husaini Yusuf Bosso ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
Alhaji Husaini yace yanzu haka yan bangar sun kashe kusan mutane ashirin da daya wanda yan bangar sun kone gawarwakin su ta yadda ba za a Iya gane su ba.
Wani da abin ya shafa, Malam Muhammadu Dabo, yace an kashe tare da kone yayansa uku a Tashar Hajiya cikin karamar hukumar Mashegu wanda yan bangar ne su ka yi aika-aikar.
Da yaje bayani a madadin kungiyar yan bangar a jihar Neja, jigo a kungiyar Ahmed Gwani yace wannan gutsiri tsoma ce domin jami’an sintiri masu bin doka ne ba zai yi wu su rika daukar irin wannan hukuncin a hannunsu ba.
Da yake bayani ga manema labarai, sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Ibrahim Matane yace gwamnati na bincike kan lamarin domin samun hakikanin abinda ya faru, domin gwamnati na bin duk hanyoyin da suka kamata wajen samun zaman lafiya a jihar.
Rahotannin dai sun tabbatar da yawan Fulani makiyaya na kauracewa zuwa makotan jahohi saboda tsoron hare-haren da ake kai masu a matsugunnan su, wanda an kai ga kashe da dama daga cikin makiyaya a sassan jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *