An haifi yarinya mai hanci daya  a garin Bunu cikin karamar hukumar Rijau a jihar Neja.

Yarin tana cikin koshin lafiya a lokacin da wakilinmu ya yi kicibis da yarinyar sai dai bai samu sararin da zai magana da mahaifan yarinyar domin sanin halin da ake ciki da shawarwarin da suka samu kan wannan ‘ya ta su.

Managarciya na ganin yakamata a kai yarinyar asibiti domin samun shawara ko matakin da za a iya dauka da sauri game da yarinyar.

Wannan karin da aka gani saman idonta da kussuwa mai kama da ta hanci a lokaci daya kuma in da hanci yake kussuwa daya ce a bude daya na rufe hakan abin al’ajabi ne da neman shawarar masana kan matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *