Tambuwal ya kafa kwamitin  da za su ƙididdige hasara kan gobar Kasuwar Sakkwato
Muhammad M. Nasir
Da safiyar ranar Talata aka tashi da gobara a babbar kasuwar Sakkwato in da wutar takwashe sama da awa 9 tana ci da wuta, bayan zuwan gwamna a wurin ya ba da sanarwar kafa wani kwamiti da zai binciko musabbabin tashin gobarar da abin da ya kamata gwamnatin jiha ta yi
Gwamnan ya dawo Sakkwato kusan awa biyar da tashin gobarar, kai tsaye ya tafi kasuwar don ganewa idonsa anan ne ya kafa kwamitin ya ce za a ƙaddamar da shi ba da jimawa ba.
Kwamitin na ƙarƙashin jagorancin Mataimakin gwamna
Manir Muhammad Dan’Iya da mambobinsa kwamishinan filaye da gidaje da kwamishinan ciniki da shugaban kwamitin ciniki a majalisar dokokin jiha.
Sauran su ne Alhaji Ibrahim Milgoma da shugaban ‘yan kasuwa na babbar kasuwar Alhaji Abubakar Altine  da Malam Bello Yabo da Namadina Abdurrahman.
Kwamitin za su gano yawan hasarar da aka yi da wadanda suka rasa muhallansu, da yanda za a yi don magance aukuwar haka a gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *