Spread the love
Daga M. A. Umar, Minna.
Ina mai taya Farfesa Maimuna Waziri murnar nada ta shugabar jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gashuwa.
Ina kuma taya murna ga majalisar gudanarwa ta jami’ar don tabbatar da nadin shugabar jami’ar ta bin hanyoyin da doka ta shimfida da nagartattar al’adar jami’a ba tare da wata hatsaniya ba.
Wannan bayanin na kunshe ne a wata takardar sanarwar manema labarai da shugaban majalisar ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Abuja lahadin nan mai karewa.
Takardar sanarwar ta cigaba da cewar da wannan nadin na Farfesa Waziri, majalisar gudanarwar ta dora akan turbar da aka dora jami’ar gwamnatin tarayya, Gashua domin zama cikakkiyar cibiya ta koyon ilimi da bincike.
Farfesa Waziri ta yi aikin da kowa ya yaba a jami’oi ukku wanda suka hada jami’ar gwamnatin tarayya, Gashua inda ta rike mukamin mukaddashiyar mataimakin shugaban jami’ar har ya zuwa wannan sabon mukamin da aka nada ta.
Basirar aikinta ya bada gaggarumar gudummuwa wajen nadata a wannan mukami, da kuma bada tabbacin zata gudanar da wannnan gaggarumin aiki cikin nasara.
Nasarar Farfesa Waziri a bangaren koyarwa da shugabanci abu ne da zai zaburar da matan arewa da sauran bangarorin Nijeriya da suke da hankoron zama fitattu a cikin ayyukan su da bada kasaitattar gudummuwa ga cigaban kasa.
Ina mai bukatar ta da ta cigaba da zama abin misali ta hanyar amfani da basirar ta ta iya mulki da koyarwa a yayin da take aiki da hukumar gudanarwa da ma’aikatan jami’ar don daukaka darajar jami’ar zuwa matakin kololuwa a tsakanin jami’oin kasar nan.
Ina mai kara taya Farfesa Waziri murna da mata fatan wa’adi mai cike da nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *