Spread the love

Masarautar  Wazirin Sakkwato, ta nada Alhaji mas’ud Musa Bashar Rahamaniyya a matsayin Turakin Wazirin Sokoto.

Wannan ya na ƙunshe ne a jikin wata Sanarwa mai ɗauke da sa hannun wazirin Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu.

Kamar yanda ya ce  a sanarwar  naɗin Sarautar ya faru ne domin nuna karramawa tare da yabawa da irin gudummawar da Alhaji Mas’ud Musa Bashir ke bawa masarautar wazirin sokoto, da al’ummar musulmi baki ɗaya.

Haka zalika farfesa, ya bayyan cewa bukin naɗin Sarautar zai gudana a lokacin da ya dace.

Shi dai sabon Turakin wazirin ɗan kimanin shekara 32 ne , an haifeshi a Jihar sokoto, inda yake zaune a unguwar Sama Road dake Sokoto.

Matashin gwargwado yana samun yabo a tsakanin matasa kan tallafin da yake ba su.

 

A ɓangaren kasuwancinsa, shi ne babban Manajan Darakta a Kamfanin Al’mas’ud Oil and Gas a lokaci guda Kuma Manajan Darakta na Ɗan Musa foundation.

Shafiu Garba Reporter

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *