Spread the love
Ba Wata Kotun Da Ta Yanke Hukuncin Da Kafafen Yada Labarai Ke Yadawa- Yanga
Daga M. A. Umar, Minna
An yi kira ga gwamnatin Neja da ta sanya idanu akan abubuwan da ke faruwa a ma’aikatar filaye da gidaje da hukumar kula da tsarin gari kan yadda suke wuce gona da iri a ayyukan su. Alhaji Hamza Yanga Buba ne yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna.
Alhaji Hamza ya ce kusan duk rigingimun da wadannan ma’aikatan ke yi da sunan gwamnati, harƙalla ce kawai suke yi da haɗa kawunan jama’a akan filayen su. Ban san wata doka a jihar nan da ta baiwa ma’aikacin Urban ko Land and Housing damar zama dillalin filaye ko gidaje ba a gwamnatance, da zai ba su damar fakewa suna shiga unguwanni suna sayar da filaye ba.
Yanzu abin mamaki ma da ya faru, suna yaɗa labarai a kafafen yaɗa labarai masu zaman kan su da sunan wai kotu ta haramta min yin iko da duk wani abu da ya shafi unguwar Brighter, wanda wannan kuskuren fahimtar hukuncin kotun ne, domin alkali Mika’ilu mai shari’a a babban kotun ta hudu ya kori karar  ‘yan sanda kan kama ni da suke yi, amma maganar ban da wani hakki a Brighter ba gaskiya ba ne.
Duk wanda ya mallaki fili a Abdussalam garage, ko Farm center ko 119 ni na sanya mai hannu, saboda haka masu fakewa da sunan masarautar Minna ko gwamnatin jiha mun san su kuma suna fakewa ne da su dan bata masu suna.
Mai alfarma sarkin Minna, ba wanda zai shiga tsakanin mu, suna anfani da sunan sa dan su bata shi, mun sam masu zuwa da takardu da sunan masarauta, na fito ne dan in kare mutuncin sarki kuma shi mai martaba shaida ne, dan haka ina kira ga maigirma gwamnan jiha, Alhaji Abubakar Sani Bello, kasancewar sa mai hakuri da hangen nesa, da ya sani idan bai taka burki ga ‘yan Urban da Land and Housing ba, ba za su daina hada rikicin filaye a jihar nan ba.
Da ya juya kan tsaro kuwa, dattijon ya yabawa gwamnan kan goyon bayan da yake baiwa kwamitin tsaron unguwanni, wanda hakan ya taimaka gaya wajen dakile bata garin da ke fakewa cikin al’umma. Domin da daman unguwannin da ake samun rahotannin sace-sace da aikata muyagun ayyuka an baiwa wadannan jama’ar damar kare kawunan su.
Yana da kyau yadda gwamnati ke hada goyon baya su kuma jami’an tsaro na tallafawa, jama’a su kara kaimi wajen karfafa shirin dan kawo karshen bata garin da ke fakewa a cikin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *