Spread the love
Wani sirri da ya bayyana bayan rasuwar  kwamishinan Tambuwal  mai shekara 64

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya rasa daya daga cikin kwamishinoninsa Alhaji Abdulkadir Jeli Abubakar da marecen Alhamis ya bar duniya yana da shekara 64 bayan doguwar jinya.
Kwamishina ne a ma’aikatar cikin gida  ya rasu bayan wata bakwai da rasuwar kwamishinan ma’aikatar filaye da gidaje  Surajo Gatawa.
Margayin kane ne ga Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bar mata biyu da diya da jikoki.
An yi masa sutura kamar yadda shari’ar musulunci ta shardanta, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yana cikin wadanda suka halarci sallar janaza margayin.
Bayan rasuwar margayin mutane da dama sun fitar da wani sirri  kan margayin da yake shi rayuwarsa ta duniya.
Waɗanda suka san margiyin sun bayyana cewa shi mutum ne mai haƙuri da juriya kan kowane lamari, yana kawaici da kawar da kai ga abin da bai shafe sa ba kuma shi mutum ne tsantseni ga duk lamarin da ya shiga cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *