Spread the love
Shirin samarwa matasa 774,000 aiki zai rage raɗaɗin talaucin da ake fama da shi a Nijeriya—Malami
Daga Muhammad M. Nasir
Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana shirin samar da aiki ga matasa   774,00 wani ɓangare ne na fito da hanyoyin rage rashin aikin yi ga matasa da matsalar tsaro da ke addabar wasu yankunan Nijeriya.
Malami ya faɗi haka a Birnin Kebbi lokacin da yake ƙaddamar da shirin a jihar ya tabbatar da samar da aikin yi na cikin abubuwan da aka aminta za su haɓaka tattalin arziki da tayar da komaɗarsa a tsarin da aka yi(2017-2020)
 Bayanan sun fito ne daga mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai na Minista Dakta Umar Jibrilu Gwandu wanda Managarciya ta samu a ranar Assabar.
Malami ya ce manufar  shirin ya samar da aikin yi da tafiya da al’umma bai ɗaya, kawar da yunwa ga talakawa da kawar da talauci da inganta muhali da kawar da zaman kashe wando.
Minista ya ce shirin a ƙaddamar da shi a jihohi takwas da zimmar samar da aikin yi ga mutum 774,000 a ƙananan hukumomi 774 anan ne za a riƙa aiyukkan da za a ayyana masu.
Ya ce matasa dubu 21 za su amfana da shirin a jihar Kebbi.
“Na gansu shirin zai bayar da gudunmuwar rage rashin aikin yi a tsakanin matasa, bayan wannan matasan da suka amfana da shirin suna iya amfani da ilmi da horon  da suka samu su zama masu dogaro da kansu” a cewasa.
Ministan ya lissafo wasu shiraruwa na gwamnatin tarayya kamar N-Power, Anchor, wanda ya tallafi manoman shinkafa sama da 2000,  ba da tallafi ga marasa ƙarfi, bayar da bashi na musamman ga ƙanana da matsaƙaitan ‘yan kasuwa da sauransu, duk dai don a haɓaka tattalin arzikin talakkawan Nijiriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *