Spread the love
Daga Muhammad M. Nasir
Fasoticin takarar shugaban kasa masu dauke da hoton Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal sun bayyana a Sakkwato.
Waƙilin Managarciya ya yi ciɓis da Fastocin Tambuwal kan shataletalen hanyar Garba Duba a birnin Sakkwato, in da aka laƙa hotunan a ko’ina.
Tambuwal dai an dade ana yi masa hasashen yin takarar shugaban kasar Nijeriya a 2023.
A kwanan baya ma ya ƙarya ta zancen da ke yawo cewa ya ayyana zai yi takarar, abin da ake kallo ya yi haka ne domin lokaci bai yi ba.
Kwatsam sai ga wasu magoya bayansa sun yi masa fostar tare da laƙawa a ɗaya daga cikin kaya mallakar gwamnati.
A ranar Alhamis ne data gabata Managarciya ta ga hotunan da ke nuna sha’awar gwamna da yin takarar shugaban kasa.
Managarciya ta so jin ta bakin gwamna Tambuwal kan ko yana da masaniya da fostar, amma haƙar ba ta cimma ruwa ba, duk yunkurin jin ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Muhammad Bello abin ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *