Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Jam’iyar APC a jihar Sakkwato tana kara samun rabuwar kai da shiga cikin rikici in da wasu magoya bayanta suka yi taro don kara inganta tafiyarsu da suka kira ta tsamo jihar Sakkwato.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A wurin taron dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela Dakta Abdullahi Balarabe Salame ya yi shagube mai kama da aika sako ga jagoran tafiyar APC a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko in da yake cewa “ba mu yarda wani ya shiga cikin daki ya nada mana mutane, in zai yi nadin ma ba Allah da annabi yake sanyawa a gaba ba, bisa ga son rai, kai ba malamin addini ba, ba ka bi ka’idar bature ba ka nada wane saboda biyan bukatarka.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

“Sakkwato duk wanda ya dauki kansa wani abu, ba mu dauke shi komai ba in bai son gaskiya, an ce muna rashin kunya da jayayya da wane, ba mu jayayya da jidali da kowa don ba mu san wanda ya isa a ja da shi ba, in abun da muke a kai na fada da azalumi da wanda baya son adalci shi ne jayayya, don muna son a yi gaskiya, duk wanda ya ce ba zai yi wa Sakkwato adalci, ba zai yi mana ba, bai yarda da Allah ya baiwa mutane hankali da lura ya mutunta mu ya mayar da mu mutane.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kai da ba ka wuce ba mu shekara 6 ba ka ce kai za ka shiga cikin gida ka ce a yi wane, to ni ban mutuwa ina haka nan nakai karshe.” a cewar Honarabul Salame.

Ya yi kira ga magoya bayansa su yi rijistar jam’iya kar su bari a sa musu wanda ba su so, kuma su zabi mutane nagari dake da kwarewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *