Spread the love

HUKUMAR ZABE MAI ZAMAN KANTA TA JAHAR SAKWATO TA FITAR DA JADAWALIN ZABEN KANANAN HUKUMOMIN 23 DAKE JAHAR SOKOTO.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta mallakar jihar Sakkwato ta fitar da sanarwa, Mai ɗauke da sa hannun Sakataren Hukamar Alhaji Isiyaku Garba Goronyo wadda hukumar ta aikawa ofisoshin ‘yan Jarida dake ciki da zagayen jahar Sokoto.

A cewar Sakataren  hukumar za ta fara sayar da takardun cikewa don samun  damar tsayawa takara ga dukkan ‘yan takarar da aka tsayar a ƙarƙashin jami’iyyunsu na siyasa daga ranar 1 Fabarairu zuwa 15 ga wannan shekarar ta 2021.

Bayanin  ofishin sakataren hukamar dake da mazauni a cikin hidikwatar hukumar zaɓe, a unguwar Mabera, a matsayin tsayayyen wajan da za a sayar da fom ga dukkan ‘yan takarar Kama daga chiyamomi har Kansiloli. daga misalin karfe 8:00 na safe har zuwa 4:00 na marece ko wace Rana.

 

Sakataren ya ƙara da cewa ana buƙatar kowane ɗan takara da ya yi hanzarin mayar da form dinsa zuwa wajan da ya saya, kar ya wuce ranar 28 ga watan Fabarairu, kasancewar ita ce ranar karshe ta karɓa.

An Kuma bayyana ranar 27 ga watan 3 a matsayin Ranar da za a gudanar da zaɓen.

Bayan fitar wannan jadawalin ya nuna jam’iyyun za su soma neman jama’a kenan kafin ranar zaɓe.

Jam’iyun PDP da APC ne mafi ƙarfi a jihar kuma su ne za su fafata a zaɓen in har jam’iyar adawa ta shiga zaɓen.

Shafiu Garba Reporter, Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *