Spread the love

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri.

Bisa zargin tsarewa ba bisa ka’ida ba, ya sa an maka shugaban sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, babban kwamandan rundunar sojojin yanki ta bakwai (General Officer Commanding 7 Division) tare da babban Antoni na Kasa kuma ministan shari’a ta Nijeriya, a babbar kotun Nijeriya (Federal High Court) dake Maiduguri bisa zargin tsarewa ba bisa ka’ida ba.


Takardar karar mai dauke da lamba. FHC/MU/CS/1/2021 wadda Alhaji Ibrahim Shehu Damakosu da Sabo Yahaya suka shigar a gaban kotun tare da gabatar da bukatar kotun ta bi musu hakkinsu na dan Adam kamar yadda sashe na 46 (3) ya nuna a kundin tsarin mulki na 1999; wanda aka yi wa gyaran fuska.


A bukatar masu korafin sun kwarmata cewa an garkame su ne a wajen da ake kulle mutane a barikin sojojin Nijeriya ta bakwai (7 Division, Nigerian Army) a Maimalari Cantonement, dake birnin Maiduguri daga 24 ga watan Nuwamban 2020 har zuwa yau, ba tare da gabatar da su a gaban kotun da ta cancanta ba domin tuhuma, wanda hakan ya saba da dokokin kasa, kuma ya sabawa ka’idar da doka ta shata.

Saboda haka sun bukaci kotun ta tilasta wa wadanda suke karar su gabatar da su gaban kotun da ta dace domin tuhuma nan take daga tsarewar da ake musu ba bisa kan doka ba.

Bugu da kari kuma, sun nemi a biya su diyyar naira miliyan 100 tare da neman afuwarsu a rubuce da wani umurnin kotu saboda nan gaba idan bukatar hakan ta taso.
Bayan shigar da karar ba a sanya lokacin sauraron karar ba domin duba korafinsu bisa daidai da tsarin tanadin doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *