Daga Aminu Abdullahi Gusau.
Hukumar kashe gobara ta jihar Zamfara tace ta samu nasarar dakile hadarin gobara a fadin jihar Zamfara har guda  767, a shekarar da ta gabata watau  2020.
Mu kaddashin Daraktan hukumar, Abdullahi Jibo Dauran ne bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labari a Gusau babban birnin jiha, inda yace duk rahotan nin da suka samu na gobara a kanannan hukumomi  sun samu nasarar dakile su.

Ya bada kididdigar gobarar kamar haka, a garin Gusau an samu tashin gobara 237, sai kuma Kaura Namoda 116, Talata Mafara 112, Tsafe 85 da Gummi 77.
Sauran sun hada da karamar hukumar mulkin  Anka inda sukeda tashin gobara  56,  Shinkafi 36, Bungudu 32, Maru da  Bakura suna da tashin gobara 28, dukan su. Sai kuma kauyen  Nasarawa sunada 13,  Birnin Magaji 11, hakazalika  Maradun, Jangebe da  Kasuwar Daji kowanen su nada tashin gobara 10.  Zurmi nada 8, Dansadau 6 da kuma Bukkuyum dake da 4.

“Gaskiya shekarar data gabata anfi samun hadarin gobara, wanda hakan baya rasa nasaba da halin ko inkula da mutane ke nunawa wajen mu’amala da kayan lantarki dake gidajen su”. inji shi.
Mu kaddashin Daraktan ya kara da cewa mutane basu kiyaye shawar warin da ake basu ta yadda zasuyi aiki da wutar lantarki a gidajen su da kuma wajen kasuwan cinsu, domin a hana yawai tar samun hadarin gobara.

Daga nan sai yayi kira ga jama’ar wannan jihar dasu guje wa yin duk abinda zai kawo hadarin gobara, hakama yayi kira ga hukumar kasuwar jihar Zamfara dasu tilas tawa yan kasuwa sayen kayan kashe gobara a shagunan su dake ciki da wajen kasuwar.
Daga karshe ya yabawa gwamna Bello Muhammed Matawalle bisa ga namijin kokarin da yayi na samar masu da motocin kashe gobara a duk fadin jihar, inda yace kananan hukumomi 14 da ake dasu suna da motocin kashe gobara, had da kari ga kauyukkan dake da nisa da hedikwatar karamar hukumar mulkin su.
Ya kara da cewa, a wannan mulkin sun samu kyakkyawar kulawa inda yanzu haka hukumar tanada ma’aikan da suka kai kimanin 600, a cikin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *