Daga Muhammad M. Nasir.

“Duk da ni dan jam’iyar APC ne abin da ke faruwa a kasar nan yana damuna talaka a Arewacin Nijeriya yana kukan harkar tsaro muna rokon Allah ya kawo mana gyara, kasa na cikin wani hali har dai a Arewa kwana a gida yana yi wa mutum wahala, an roki shugaba Buhari ya sauya hafsoshin tsaronsa ya ki, ko bai jiya ba ne ko kaka na kasa ganewa, shin mine ne suke yi masa wanda shi kadai ke ganinsa sabanin abin da mutane ke gani.”

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Honarabul Umar Ibrahim Atakonyo jigo ne a jam’iyar APC a jihar Sakkwato shi ne ya furta hakan a zantawarsa da manema labarai a satin da yagaba ya ce ba su kadai ne masu basira ba duk abin da mutum ke yi ba a ga canji ba ana gwada wani, ina jami’an tsaro, ‘sai mu ga kamar da hadin bakinsu ne don in da diyansu ne ke shiga matsaloli da an dauki mataki, wace irin rayuwa ce ba tausayi a zukatan shugabanni’.

Honarabul ya yi kira ga shugaba Buhari ya sallami wadanda ke zagaye da shi ya dauki wasu mutane don na kwarai ba su karewa a jingine komai a ceci talaka a wannan hali na kaskanci.

Haka ma ya soki gwamnatin Tambuwal ya ce ba ta da wani aikin kirki da za ta nuna farfaganda ce kawai ta cika da ita, “Tambuwal dan siyasar Abuja ne hakan ya sa bai rike mutane yanda yakamata ba, bai damu da halin da al’umma suke ciki ba, ko ba a fada masa gaskiya ko baya dauka a siyasar Sakkwato ba a samu dan siyasar da ya yaudari mutane kamarsa ba.” cewar Honarabul Atakonyo.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Honarabul ya ce shi a shekarar 2023 yana goyon bayan takarar Honarabul Abdullahi Balarabe Salame ya zama gwamnan Sakkwato don kawo sauyi mai alfanu a jihar.
“Salame jajirtacce ne dake son cigaban al’ummarsa in ya samu nasara zai ciyar da Sakkwato gaba ta fannonin rayuwa don kara bunkasa tattalin arzikin jiha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *