Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya taya murna ga Ambasada Faruk Malami Yabo Kan nada shi jekada da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi a kasar Jordan.

Sanata Wamakko ya bayyana cewa tura Faruk Yabo a kasar Jordan domin aikin jekadanci abu ne Mai kyau ga Nijeriya.

Wamakko wanda yake tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ne, ya nuna jindadinsa na ganin an tura Faruk Yabo daya daga cikin manyan kasashen Gabas ta tsakiya waton kasar Jordan, lura da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na aiki sosai wajen ganin ya maido da Martabar Nijeriya.

Wamakko ya yi hasashen zuwan Ambasada Faruk Yabo a kasar Jordan zai Kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen guda biyu.

Sanata Wamakko a bayanin da ya fitar ta hannun mataimaki na musamman a bangaren yada labarai Bashir Rabe Mani ya ce sabon jekadan zai baiwa marada kunya, kan sanin kwarewa da gogewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *