Spread the love

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da ‘ya’yan jigo a jam’iyyar APC bangaren sanata Kabru Marafa, a karamar hukumar mulkin Maru Alhaji Sani Gyare Kadauri, sun bukaci a ba da kudin fansa har naira miliyan hamsin(N50M), idan dai har yana son a sako su yaran guda shida.
A ranar jumu’a da ta gabata ne ‘yan bindigar suka shiga kauyen kadauri dake gundumar Jabaka a karamar hukumar mulkin ta Maru, suka yi awon gaba da ‘ya’yan shugaban su 6 da kuma wata yarinya diyar abokinsa.

Da yake yiwa manema labarai  bayani halin da ake ciki game da ko masu garkuwa da yaran nasa sun kira  shi domin tattaunawa, Alhaji Sani Gyare ya ce, ‘yan bindigar sun kira shi suka fada masa cewa, ya basu kudi ko kuma yayi hasarar ‘ya’yansa.
“Wallahi sun kira ni suka ce in biya kudin da suka fada man watau miliyan hamsin, domin su sako man ‘ya’yana, in ba haka ba za su kashe su batare da  bata lokaci ba”. inji Gyare.

Da aka tambaye shi ko ya sanar da hukumomin  da ya kamata su san halin da ake ciki, sai ya ce a’a babu dole da ya sanar da su saboda tun lokacin da wannan bala’i ya same shi babu wanda ya tausaya mashi, duk da yake sun san abin da ya faru gare shi.
Ya kara da cewa duk da sakataren gwamnatin jihar Zamfara Alhaji Bala Bello Maru, wanda suka fito karamar hukumar mulkin daya da shi, tun ranar da abun ya faru bai zo ba kuma bai kira shi ba domin ya jajanta masa.
Gyare ya kara da cewa shugaban karamar hukumar mulkin Maru, Alhaji Salisu Isah Dangulbi, shi ma bai kira shi ba ko ya aika mashi da sakon jaje bisa  ga wannan iftila’i da ya same shi.

A don haka ya nuna rashin jin dadinsa, ya ce haka yake ji kamar shi ba dan gida ba ne, kuma yanzu bai san abin da zai yi ba, saboda shi dai bayada wadannan makudan kudaden da ake bukata kafin a sako masa ‘ya’yansa.
Ya ce bayan da zai iya hada miliyan hamsin, in duk ya sayar da dukiyar da ya mallaka, kuma ya fada ma masu garkuwa da yaran haka, amma sai suka dinga yi masa dariya  kawai a cikin wayar salular da suka kira shi.
Daga nan ne sai yayi kira ga gwamnatin jihar Zamfara data tarayya dasu kawo mashi dauki domin a kubutar da yayan nasa ga hannun ‘yan ta’ddan dake garkuwa da su.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Mohammed Shehu, ya ce suna da masaniyar cewa an sace yara a Kadauri, amma basu da labarin maganar biyan kudin fansa da ‘yan bindigar suka bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *