Spread the love

Karatun littafan soyayya novels ko kuma dogaro da su a matsayin wani tsani wanda zai iya taimaka ma uwargida ko amaryar da ke shirin yin aure ko take cikin rayuwar auren,cigaba ne irin na mai hakar rijiya.
Saboda duk wani abu da marubuciyar novels za ta rubuta kashi 90% babu shi a wannan doron duniyar tamu,rayuwa ce za ta dauko mai shige da rayuwar aljannah.

Abind yasa na ce haka,su wadannan littafan ba su kawo ainihin hakikanin zamantakewar aure a kasar hausa.

Cikin kashi dari na matsalolin aure da ake fuskanta cikin gidaddajen ma’aurata,basu tabo matsala talatin su fade ta.
Bance littafan basu taimakawa ba, amma rashin amfanin su yafi amfanin su yawa ga al’umma.

Mudai abinda muka sa ni ko mu ka ji labari ga iyayen mu da kakannin mu,ko sadda duniya na zaune kalau, mata na girmama mazajensu, suna tsoron maza ainun,suna soyayyar su daidai tunanin su,suma mazan na kyautatawa matan sosai tare da jin tausayinsu.

Amma ba mu ji labarin abin da ake rubutawa ba daga bakin su

Littafan NOVELS A NAWA TUNANIN ZA’A IYA CE MUSU TAMBAYA DABAN AMSA DABAN, KO KUMA CIWO DABAN MAGANIN DA AKE SHA DABAN!

Wannan al’ummar ba ta bukatar a koyar da ita soyayya irin ta ALJANNU, ko kuma a fada ma ta zamantakewar da babu ta;

Duk matar da ta dogara ga wadannan littafan domin tsintar darasi tana cikin matsala

Duk yarinyar da ke shirin yin aure ta dauki rayuwar novels to ta rumfo,saboda za taje da tunani jin irin dadin da ta gani acikin littafan.

Abinda muka sa ni ga al’adar bahause ko kuma zuciya irin ta namiji,duk laifin da yayiwa matar sa komai girman sa, bazai shiga damuwar da ake bayyanawa namijin novels ya shiga ba.

Acikin novels za ka ji wai namiji ya samu matsala da matar sa yazo ya girke gabanta yana kuka tare da magiyar tayi hakuri,wani lokacin za kaji har ya kwanto asibiti akan wannan matsalar.

Kamata yayi ga wadannan marubutan su fantsama acikin al’umma domin su san matsalolin aure,sannan su zo su rubuta.

Allah yasa mu gane.

Zainab Aliyu sifawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *