Spread the love

Daga Mohammad M. Nasir

Hukumar shirya jarabawa ta kasar Nijeriya waton NECO ta fitar da sakamakon jarabawar daliban makarantun sakandire a kasar SSCE.

Sakamakon ya nuna an samu karuwar kashi biyu cikin dari na yawan wanda suka samu maki biyar zuwa sama a dukkan jarabawar hakan ke nuna an samu nasarar jarabawar a wannan shekarar.

Magatakardan Hukumar, Farfesa Godswill Obioma ne, ya sanar da hakan a hedikwatar hukumar dake garin na Minna a jihar Neja.

Hukumar ta NECO ta soke sakamakon makarantun sikandare 12 saboda an same su da aikata satar amsar jarabawa a lokacin gudanar ita wanda hakan ya sabawa dokar zana jarabawa a kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *