Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir

Shugaban cibiyar kula da cirutoci a Nijeriya NCDC ya gargadi ma’aikatan lafiya da su rika kula da cutar Korona a lokacin da suke duba marar lafiya dake fama da Masassara ko cizon sauro.
Babban daraktan Dakta Chikwe Ihekweazu ya ce suna cikin dari-dari don kasar ta shiga mawuyacin hali in da asibitocinsu da kayan aikin da suke da su a kasa ba su iya wadatar da mutaanen da ke dauke da cutar Korona a Nijeriya.
A cewarsa hakan na iya sanya ma’aikatan lafiya daukar mataki mai tsauri kan sha’anin.
Dakta ya sanar da gargadin ne a Abuja lokacin da yake yi wa kwamitin kula ciwon Korona na kasa a Abuja ya yi kira gare su da su yi tsayin daka a samar da mafita kan COVID-19.
Cibiyar ta bayar da labarin ‘yan Nijeriya dubu 100 ne aka tabbatar suna fama da cutar Korona, abin da ke nuna cewa kwayar cutar ta shafi sama da mutum 100,000 kenan, sama da mutane 1300 suka mutu a cikin wata 11, sai miliyoyi a duniya.
Ya ce mutanen da ke shirya taron al’umma suna sanya kansu da bakinsu cikin hadari, wadanda ba su shiga cikin rugutsimin mutane sun tsira.
Matasa masu zuwa wurin raye-raye suna sanya uwayensu cikin hadari, domin duk in da aka ce ana fama da cutar a cikin mutane, sama da mutum 100 ya mutu dubi wannan kididdigar yakamata al’umma su tashi tsaye wajen kare kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *