Spread the love

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu a bayanin da ya fitar yake cewa, bayar da wa’adi da wata kungiya dake Sakkwato majalisar hadin guiwar musulmai na kira ga Matthew Hassan Kukah na bayar da hankuri ga musulmai kan maganar da ya yi na cin zarafin musulunci ko yabar jihar Sakkwato.
Ya ce hakan kuskure ne domin ya sabawa kundin tsarin kasar Nijeriya.
Malam Garba ya ce kundin tsarin kasa ya bayar da damar fadin albarkacin baki ya kuma ba da damar ɗan ƙasa mallaki gida da zama a duk in da yake so a cikin kasa, tsarin mulki bai yi sakaci da sanin bambancin addinai ba, nauyi ne ga kowace gwamnati musamman ta dimukuradiyya ta kare martabar tsarin kasa.
A jiya ne majalisar dake jihar Sakkwato ta fitar bayanin ga manema labarai abin da fadar shugaban ƙasa suke ganin kuskure ne suka yi, domin tsarin mulki ya baiwa Bishop damar abin da ya aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *