Spread the love

Tsohon Gwamnan Kano Kontogora ya Kwanta Dama

Daga M. A. Umar, Minna

A yau ne Allah ya dauki rayuwar Kanal Aminu Isah Kontagora, marigayin ya taba zama gwamnan jihar Kano inda daga bisani kuma ya sake zama gwamnan jihar Binuwai.
Marigayi Kanal Aminu Isah Kontagora, ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya.
Da yake karin haske ga wakilinmu, wani makusancin marigayin, Dakta Hassan Tagwai Zaki, mamallakin wani asibiti mai zaman kanta Kontagora Clinic, ya ce tabbas yaji wannan mutuwar, domin marigayi Kanal Aminu Isah Kontagora, mutumin kirki ne da jihar Neja ta rasa.
Marigayin wanda ya taba yunkurin fitowa takarar gwamnan Neja a jam’iyyar PDP a shekarar 2019, ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan ‘yan siyasa wajen ganin an yi zabe mai tsafta a jihar nan musamman a yankin Neja ta arewa.
Fadar shugaban kasa da gwamnatin Neja na daga cikin sahun gaba wajen yin ta’aziyya ga iyalan mamacin da al’ummar jiha baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *