Spread the love

Tambuwal ya ƙaddamar da kwamitin da zai bashi shawara kan mayar da COE jami’a

Daga Muhammad M. Nasir

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kafa kwamitin mutum 17 da za su bashi shawara kan mayar da kwalejin ilmi ta Shehu Shagari jami’ar ilmi a Sakkwato.

Kwamitin zai yi aiki karkashin kulawar mataimakin shugaban jami’a mallakar jiha Farfesa Muhammad Zayyan Umar nan ba da jimawa ba Gwamna zai ƙaddamar da su.
Mambobin kwamitin sun hada da Farfesa A. A. Bagudo, Abubakar Umar Dikko, Malami Umar Tambuwal, Nasiru Gatawa, da Mansur Ibrahim (Mni) dukansu a jami’ar Usman Danfodiyo suke karantarwa.

Sauran su ne Dakta Mansur Isa Buhari, Malam Abubakar Usman, Mallam Muhammad Kakale Jabo da Rilwan Muhammad sai Malam Sani Sahabi Bodinga dake jami’a mallakar jiha.

Farfesa Aminu Abubakar, shugaban kwalejin gona dake Wurno da Dakta Muhammad Wadata Hakimi, shugaban SSCOE da Pharmacist Abdulmustapa Othman Ali babban sakatare a ma’aikatar ilmi mai zurfi ta jiha.

Dakta Amamatu Yusuf, Dakta Nasiru Daniya, sai Kabir Umar Imam wanda zai zama sakataren kwamitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *