Spread the love

Muhammad M. Nasir.

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a jiya Lahadi ya cika shekara 55 da haihuwa rana mai muhimmanci gare shi da iyalansa da duk wani masoyinsa.
Gwamna Tambuwal wannan lokacin yana bukatar sadaukarwa da bayyana cewa shi jagora ne da ya amfanar da duk wani makusancinsa musamman wanda yake rike da abin hannunsa a cikin gwamnati yake ko shi dan siyasa ne ko dan kasuwa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A yanda abubuwa ke tafiya ana hasashen Tambuwal zai nemi tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 wannan ne ya jawo hankalin Managarciya ga bibiyar manyan jaridun Nijeriya a jiya Lahadi da Tambuwal ke murnar zagayowar shekarar haihuwarsa domin ganin irin cire shi kunya da nuna sadaukarwar da mukarabansa za su yi wanda hakan tura sako ne ga duk wani mai son yin jayayya da Tambuwal a wurin neman a tsayar da shi takara, cewa jagoransu yana da masu kashe masa kunya da shirin sadaukarwa gare shi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kash! Sai dai hakan ba ta samu ba domin sun nuna abin da suka samu karkashinsa nasu ne da iyalansu, shi ko da yake neman takarar shugaban kasa ya nemawa kansa masu sadukarwa irin wadda ake kallo tana kama da yin hasara a buga talla a jarida.
Mataimakin gwamna da Sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan jiha dana fadar gwamnati, ba su sanya taya murna a jaridu ba.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kwamishinoni 26 daya ne kawai waton kwamishinan lafiya ya sanya tallar a jaridar daily trust.
Shuhaban jami’a mallakar jiha da makarantar kimiya da fasaha ta Ummaru Ali Shinkafi sun sanya taya murna ga gwamna sanin muhimmancin hakan yana da nasaba da jagororin shaihunnan malamai ne.
Masu baiwa gwamna shawara da mataimaka na musamman da manyan daraktoci da manyan sakatarori da kake kallon kansu ma’aikatan gwamnati dukansu ba su yarda da hasarar taya murna ga Tambuwal a jarida ba.
Kakakin majalisa dake iya baiwa mawaki mota a gaban Tambuwal kila bai fahimci aika sakon nuna tare ga Gwamna a wurin abokan adawa da hamayarsa a jihohin Nijeriya yafi muhimmanci kan ba da mota ba.
‘Yan majalisar jiha da tarayya sun kasa su yi ko da karo-karo ne su nunawa duniyar siyasar Nijeriya Tambuwal na da masu kara haskaka siyasarsa, ciki har da wadanda ya yi wa riga da wando sun ki tun da ba saka hannun jari ne ba, da zai hauhauwa bayan sauka kujera a rika diba ana ci.
Jam’iyar PDP reshen Sakkwato sun bi sahu wajen kin sa hannu a haskaka tafiyar Tambuwal a wannan lokaci da ake bukatar sanyawa tafiyar fetur da zai kara kunna wutar nasarar neman shugaban kasa.
Managarciya ta fahimci da yawan mukaraban Tambuwal sun san muhimmacin taya shi murnar sun dai ki yi ne a dalilin rowa da ta mamaye zukatansu, wasu daga cikinsu magoya bayansu sun rika yawo da tallar taya murnar da suka yi a kafar sadarwa ta facebook domin haka ne mafi arha a yadawa, domin duk yanda aka yi maka tsada 1000 ta isa.
A lokacin da Tambuwal ke zagaye Nijeriya wajen gaisuwar Ta’aziya da bude aiyukka da wasu muhimman tarukka, amma mukarabansa sun kasa aikawa muhimman mutanen da yake zuwa wajensu sakon cewa muna tare da namu ku kara goya masa baya. Wannan abin takaici ne ya faru, matukar Tambuwal bai samu damar zama shugaban kasa ba wannan ranar da mukarabansa suka kasa baiwa muhimmanci ba za ta sake dawowa ba har abada.
Tambuwal ya yi shekara 55, muna fatan sake ganin wasu biyar a tare da shi ko a lokacin zai samu makusanta ba irin wadan nan ba, da za su nunawa duniya jagoranmu yakai shekara 60.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *