Spread the love

Burin jam’iyarmu samar da siyasa ba da gaba ba—-Ibrahim Mai Kassu Goronyo
Daga Muhammad M. Nasir
Shugaban jam’iyar BOOT PARTY a jihar Sakkwato Alhajji Ibrahim Mai Kassu Goronyo ya bayyana manufar jam’iyarsu a siyasar Nijeriya da jihar Sakkwato shi ne abin da ya bambanta ta da sauran jam’iyyun siyasa dake kasar nan.
Shugaban a zantawarsa da Managarciya a ofishinsa dake birnin jiha ya ce manufar jam’iyarmu samar da wani tsarin tafiyar saiyasa ba da gaba ba, bambancin jam’iya wani abu ne na ra’ayi da kowa ke da shi don ba da tashin gudunmuwa a bangaren da ya dauka.
“Mun fara tattaunawa da mutane a jiha domin kara bunkasa tafiyarmu cikin fahimta da tsari mai kyau don kawai a samar da wanzuwar tafiyar siyasa ba da gaba ba, abin da tsohon Gwamna Bafarwa ya yi na gaisuwar ta’aziya ga Wamakko abin yabawa ne domin hakan ya haifar da farinciki a tsakanin mutane, siyasa ba da gaba ba ita ce kadai za ta iya kawo canjin da ake bukata a kasar Nijeriya domin tsarin mulki ya baiwa kowa damar yin jam’iyar siysar da yake so.” A cewarsa.
Ya ce shi baya da ra’ayin da wasu ke da shi na ganin jagororin sun hada kansu ne domin yakar Tambuwal a gaba ‘Tambuwal shi ma shugaba ne da yake kula ra’ayin jama’a na daidai.
“Rijistar mambobin jam’iyarmu da za mu fara muna kira ga duk wanda zai shiga BOOT PARTY ya shiga ne don cigaban kasa da al’ummarsa.” In ji Mai Kassu Goronyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *