Spread the love

2023 BAYAN GWAMNA TAMBUWAL…..MENENE MAKOMAR SIYASARMU.

Daga Yusuf Muhammad Ladan

Ba shakka siyasar ubangida na kawo koma Baya ga harkar cigaban siyasa a kasa, jaha harma da yanki.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shi ne mutum na farko da ya fara karya Lagon siyasar ubangida a jahar Sokoto a 2019 Wanda a halin yanzu munga amfaninshi.

Siyasar ubangida na haifar da matasaloli kamar haka:

1. Bazakayi ra’ayin al’umma ba sai na ubangidanka.

2. Duk laifin da ubangida Ka ya yi bakada hurumin hukuntashi ko taka masa birki.

3. Baka da halin Gina Mutanen da suka wahala da Kai sai dai yaran ubangidanKa

4. Wasu dattawan jaha ko na kasa Basu isa su Baka shawara Ka dauka mussaman idan ubangidanka Baya Shan inuwa Daya da su.

5. Dama dai sauransu…..

A waadi na biyu na gwamnati Tambuwal an samu an yaki wannan matsala Wanda yayi sanadiyar Fara samun ayukan more rayuwa daga ciki da wajen babban birnin Sokoto.

Amma wannan matsalar ta siyasar ubangida da alamu tana batun dawowa da karfi irinna guguwa kafin ma 2023.

A jahar Sokoto muna da gidan siyasa uku inda yanzu gida guda ya ruguje sanadiyar rashin tasirin gidan a siyasance saboda wasu dalilai da bazan ambatosu nan ba.

Yanzu gida biyu ne masu karfi a siyasar jahar Sokoto a halin yanzu.

Uwayen gidajen nan guda biyu suna da karfi da kuma dukiya kuma suna a jam’iyu daban-daban Wanda dukansu Basu da buri face ace 2023 Yan gaban goshinsu su ne a madafun iko.

Shakka Babu mutane ‘Yan baruwanmu da dama damuwarsu shi ne menene makomarsu a siyasance bayan Gwamna Tambuwal a shekara ta 2023.

Dalili kuma shi ne wadannan ‘Yan siyasan gidajen nan yaransu da uwayen gidajensu su ne mafi daraja a garesu kafin sauran ‘Yan Allah gamu gareka.

Anya idan muka zabe su ba uwayen gidajen su zasu yiwa aiki ba a maimakon talakkawa.

To gaskiya idan muka gano uwayen gidajen su za su yiwa aiki kafin zaben 2023, yanada kyau muma talakkawa mu zama uwayen gidajen kanmu, mu zabo wani Wanda zai mana abunda muke so ba abun da wani yake so ba.

Inba haka ba Birnin Shehu ba za ta taba kamo kafar birnin Dabo ba.

Sako Fatan Alkhairi daga Isuhu Mamman

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *