Spread the love

Hauwa’u Salisu (Haupha)

‘Yan bindiga daɗi sun yi garkuwa da motar haya guda ɗauke da mutane 8 a cikin motar tsakanin garin Kankia da gidan mutum ɗaya wato daga Katsina zuwa Kano.

A cikin waɗanda suka ɗauke akwai wata matashiyar ‘yar kasuwa mai suna Hajiya Zulaihat wadda kasuwanci ya kai ta Kano a ranar.

Ɓarayin sun kira wayar mahaifiyarta inda suka buƙaci da a kai masu Naira Miliyan huɗu cif sannan su sako mata yarinyarta.

Sun jajjada ma mahaifiyarta cewa kuɗin kawai suke buƙata kuma babu abin da za su yi ma yarinyarta.

To yanzu dai ana ta cuku-cukun yadda miliyan huɗu zata isa ga masu garkuwa da Hajiya Zulaihat.

Barayin da sukai garkuwa da Hajiya Zulaihat sun kira wayar mahaifiyarta sun yi kashedin a daina kiran wayarta.

Sannan sun tabbatar da cewa a miliyan huɗu da suke buƙata sun samu miliyan biyu da dubu ɗari bakwai a account ɗin Hajiyar don haka cikon kuɗin suke jira sai su sako ta.

Mahaifiyar yarinyar ta tabbatar masu da cewa yarinyar marainiya ce bata da kowa sai ita don haka su gaya mata inda zata kai cikon Kuɗinsu su bata yarinyarta.

Ta ƙara da roƙonsu da don Allah ka da su taɓa mata mutuncin yarinya .

Sun amsa mata da cewar su kuɗi kawai suke amsa mace ko ta kai tsada akan kyau babu ruwansu da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *