Spread the love

Hauwa’u Salisu (Haupha)

Anyi sakin aure akan alewar Naira goma a garin Dutsanma jahar Katsina.

Labari da ɗumi-ɗuminsa, wasu kushiyoyi sun yi fadan doke-doke saboda alewar da maigidansu ya siyo ta Naira goma ya raba bai ba yarinyar amarya ba.

Hakan ya tunzura amarya har ta gaza haƙuri ta tambaye shi ko yarinyar ta shegiya ce da bai ba ta alewar ba? Shi dai maigidan sai ya fice ya bar gidan batare da ya tanka Mata ba.

Ko da fitar mijin sai uwargidan ta ɗauki sowa da ihun an hana wasu alewa nan gaba ba a san me za a hana su ba.

Daga jin haka sai amarya ta rufe uwargidan da duka wanda sai da suka yima juna jina-jina sannan amarya ta kai ƙarar uwargidan gun police station na bakin rawun ɗin Dutsanma.
Wannan abu shi ne ya fusata mijin ya kore su da takardar saki ɗai-ɗai.

Wannan lamarin akwai rashin adalcin maigida da kuma rashin hankurin matan abin da yakamata maza su kiyaye hakkin matansu su kuma matan su riƙa haƙuri.
Managarciya ta fahimci a yau aure na mutuwa ƙasar Hausa kan rashin hankuri da adalci da kuma jahilcin ma’aurata kan ilmin aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *