Spread the love

Daga Hauwa’u Salisu (Haupha)

Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta ƙarya ta labarin da ke yawo a garin na masu garkuwa da mutane sun shirya kama mutane ta hanyar motocin haya.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Gambo Isa ne ya yi Managarciya bayani a waya cewa wannan labarin bai da shi kuma ba gaskiya ba ne a halin da ake ciki ana samun nasara kan mahara ko a satin nan an saki mutane masu yawa da aka yi garkuwa da su kan haka ya yi kira ga mutane su kwantar da hankalinsu su cigaba da harkokinsu ba wata damuwa da ikon Allah.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Labarin da ke yawo shi ne Shiga motar haya ya zama tashin hankali a yankin Katsina da kewayenta.

A labaran da Managarciya ta samu, an fada mana da cewa shiga motar haya ya zama kalube ga masu tafiye-tafiye a jahar Katsina, domin an ce yanzu masu garkuwa da mutane (kidnapping) sun raba ma direbobi motoci sun ce duk wanda ya kai masu lodi uku an bar masa motar tare da wasu kuɗi masu nauyi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan labari yasa yanzu zuwa unguwa yayi wahala a jahar Katsina da kewayenta kamar yadda wasu ke faɗi.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

An ce akwai wasu mutane da suka shiga motar haya a ƙarshe dai a wurin masu garkuwa aka samo su.
Ko ya abin yake dai hukumar ‘yan sanda ta ƙaryata lamarin tare da kira ga mutane su daina yaɗa jita-jita a gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *