Spread the love

Buhari ya manta da jakadun Nijeriya 83 wata biyar da naɗa su

Muhammad M. Nasir

Jakadun Nijeriya 83 da gwamɓatin Nijeriya ta naɗa a yanzu sama da wata biyar da majalisar dattijai ta tantance su tare da tabbatar da mukamansu sai dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya manta da su.

Ba wani alamu na tura su ƙasashen da za su yi aiki kamar yadda binciken manema labarai ya nuna.

Jekadun ma’aikatan gwamnati da waɗanda ba su ba ma’aikatar ƙasashen waje ba a ga tayi wani abu ba na nuna tura su daga fadar shugaban ƙasa.

Wata majiyar ta ce Buhari ne kawai ke bayyana makomar jekadun dake jiran kama aiki.

Wata majiyar ta ce gwamnatin na jiran takardar yarjejeniya daga ƙasashen da za a tura jekadun. Takardar ke nuna ƙasar ta aminta da wanda aka tura mata, hakan ke nuna tsakanin ƙasashen akwai fahimta.

Managarciya na ganin Buhari ne ya manta da su saboda ba a taɓa ɗaukar wannan dogon lokaci bayan tantance jekadun ba su isa ƙasashen da za su yi aiki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *