Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Tambari Yabo ya rasu

Allah Ya karbi rayuwar tsohon Mataimakin shugaban ‘yan sanda AIG Tambari Yabo (Rtd).
An yi jana’izarsa da karfe 2:00 na rana a mahaifarsa dake karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato.

Gabanin ya kai mukamin Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda wato AIG, ya rike mukamin Kwamishinan ’Yan Sanda a Kaduna, Kano da Jihar Legas har sau biyu da kuma Oyo da Zamfara da Imo.
Ƙafin rasuwarsa ya shiga harkokin siyasa gadan-gadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *