Spread the love

Safiya Yusuf ‘yar wasan Hausa ce data fara tashe a shirin da ake nunuwa mai dogon zango a gidan talabijin na Arewa 24 waton kwana tasa’in, an cireta daga cikin shirin ba tare da wata sanarwa ba daily trust sun yi hira da ita don yi wa jama’a karin bayani kan dalilin cireta a rawar da take takawa na dalibar kimiya mai son zama likita, a gefe daya mahaifiyarta na fama da ciwon kafa amma duk da haka tana taimakonta ga cikar burinta, amma mahaifinta bai damu da karatun ba yafi son ta yi auren jari.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Bayan da wani bidiyon tsiraicinta ya fita a kafafen yada labarai ne ake ganin shi ne silar sauya ta a cikin shirin

Ta ce Ban ji dadin da aka sauya ni ba kuma nayi farinciki dalilin haka yadda mutane suka ta yin suka ba su son sabuwar Safara’u, ba ni nace ban sonta ba, amma naji daɗi yanda mutane ke nuna damuwarsu kan rashin ganina a cikin shirin, a lokaci daya kuma ba daɗi don ba za su sake ganina ba a cikin shirin, da yawan abubuwa sun faru na rashin fahimta abin da ya faru dai ya faru.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kan cece ku cen da ake yi kan sauya ta da aka yi ta ce “an canja ni ne saboda ban da lafiya a lokacin da ake ɗaukar shirin, an fara bani nan kan rashin lafiya ban da wani zaɓi sai kawai a canja ni a lokacin, shi ne gaskiyar magana kan sauya ni da aka yi.” a cewarta.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ta ce ta dawo Kaduna kwanaki kaɗan da suka wuce tana kan wani aiki ne ‘Ƙaddarar so’ shi ma shiri ne mai dogon zango, masoyanta su jira sake ganinta da wani abu na musamman nan ba da jimawa ba.

“Ba kawai ina fitowa a shiri mai dogon zango ne ba kadai, na dai fi son a dogon zango fiye fim.” a cewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *