Spread the love

Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al’amuran rashin da’a.

Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta kama wasu matasa 53 a tsakar birnin Kano da kewaye kakakin hukumar, Lawal Ibrahim, ya tabbatar da an kama matasan a ranar Talata data gabata da dare ya ce an kama su da laifiin ta’ammali tare da siyar da miyagun kwayoyi a jihar wanda hakan ya sabawa dokar kasa da addinin musulunci.
Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a lamido Crescent dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a kan siyar da miyagun kwayoyi.

“Wadanda ake zargin sun hada da maza 27 tare da mata 26 dukkansu masu shekaru tsakanin 17 zuwa 19 ne. Jami’anmu sun fita sintiri wurin karfe 10 na dare a can ne suka kamo mutane 53 da ake zargi,” a cewarsa.

Ibrahim ya ce, “mun gano cewa dukkansu wannan ne karonsu na farko da suka aikata laifin, don haka an yi masu nasiha tare da mika su hannun iyayensu, don su kara kula da tarbiyarsu kamar yadda addini ya tanadar.”
Kwamandan Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya ja kunnen matasan jihar da su gujewa aikata miyagun ayyuka kuma su zama ‘yan kasa nagari da su taimaki kansu da al’umma da har zai kasancewa ana iya alfahari da su a jiha da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *