Spread the love

Atiku ya taya Gwamnan Edo murnar nasarar da ya samu a Kotu

Muhammad M. Nasir

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar ya taya Fwamna Edo murnar samun nasara da ya yi a babbar kotun ƙasa dake Abuja kan ƙalubantarsa da APC ta yi kan takardunsa da ya gabatar na bugi ne.
APC ta ƙalubalance shi cewa dukan sunayen da ke saman takardunsa sun banbanta.
Alkalin kotu ya yi watsi da ƙarar da ya ce bata da tushe ko makama.
“Ina taya Gwamna Obaseki murnar nasarar da ya samu kan ƙarar da aka kai shi na satifiket nasa na jabu ne.
“Jinjina ga jam’iyarmu da mutanen jihar Edo da suka tsaya bayan gaskiya don su kare ƙuri’unsu kar maƙiya dimukuraɗiya su mayar da tafiyarsu baya.” a cewar Atiku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *