Spread the love

Anyi garkuwa da ‘ya’yan jigo jam’iyyar APC na karamar hukumar mulkin Maru bangaren Kabiru marafa har su shidda.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.

 Yan bindiga dadi sunyi garkuwa da ‘ya’yan jigo a jam’iyyar APC na  karamar hukumar mulkin Maru bangaren sanata kabiru marafa,  Alhaji Sani Gyare Kadauri, har su shidda.
 Ana dai  zargin cewa  yan bindigar da suka ki rungumar shirin sulhu da gwamnati Zamfara ta yi ne suka yi wannan aika aikar a kauyen na kadauri dake  gundumar jabaka  ta Karamar hukumar mulkin Maru dake jihar Zamfara.
Da yake yi ma ‘yan jarida bayani yanda abun ya faru, a yau jumu’a,  Alhaji Sani Gyare Kadauri yace, wadannan ‘yan ta’addan sun mamaye kauyen na Kadauri da misalin karfe biyu na safiyar jumu’a, sai suka fara zuwa gidan sa, inda suka dauki yaro shidda.
Ya kara da cewa, daga nan sai suka wuce zuwa gidan abokin sa mai suna  Alhaji Sani Yellow, suka dauki diyar sa Amina Sani Yellow daga nan sai suka gudu inda har yanzu ba’asan inda suke ba.
“Ni ina gidana na  Gusau, lokacin da suka shigo kauyenmu, ‘yan bindigar kawai sun shiga gidana ne domin yin garkuwa dani,amma hakan bata faru ba sai suka dauki ‘ya’ya na su shidda da kuma diyar abokina. inji shi.
Alhaji Sani ya kara da cewa, yan ta’addan sun harbi wani mutun mai suna  Rabi’u Dan Maidamma, wanda yanzu haka yana kwance Assibiti ana duba lafiyarsa, anan Gusau.
Haka zalika Alhaji Sani Gyare ya kara da cewa babu wani jami’in tsaro da aka tura domin  mayar da doka da oda, adon haka yayi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ta jiha dasu wa Allah su tura masu jami’an tsaro a kauyen nasu, domin su samu zaman lafiya.
“Gwamnatin tarayya da ta jihae Zamfara kuji tsoron Allah ku yi duk abinda ya kamata domin kare rayuwa da dukiyoyin jama’a” ya ce.

Idan baku manta ba shekarar da ta gabata ne gwamna Bello Muhammed Matawalle tare da taimakon tsohon kwamishan ‘yan sanda CP Usman Nagogo, suka kirkiro shirin sulhu tsakanin Fulani da Hausawa a duk fadin jihar Zamfara domin samun dawwo da zaman lafiya. Amma duk da karamcin da aka yi masu wasu daga cikin ‘yan ta’addan sunki su rungumi wannan shirin na sulhu.
Da aka tun tube shi domin karin haske game da wannan harin da akakai a kauyen na kadauri, mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara SP  Muhammad Shehu,  yace  suna jiran bayani daga jami’in Dan sanda mai kula da wannan karamar hukumar mulkin ta Maru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *