Spread the love

‘Yar kasuwa Fatima Akinpelu ta nemi kotun sasanta aure dake Mapo a ɓirnin Ibadan ta raba aurensu da ya shekara 15 da mijinta Azeez Akipelu kan zarginsa da ta yi ya so ya yi amfani da jinin al’adarta ya yi tsafi da shi.
A yanke hukunci Alkali Ademola Odunade ya zartar da hukunci raba su don bai kamata su ci gaba da zama a matsayin ma’aurata ba tun da akwai rashin fahimta a tsakaninsu.
Kotun ta bayar da umarnin fatima ta rike dansu mai shekara 14 tsohon mijin zai rika biyan 5000 kuɗin abincin yaron a duk wata.
Ya kuma nemi ya kula da karatun yaron da sauran bukatunsa.
Da farko dai Fatima ta sanya ƙarar mijin nata don tana tsoron zama da shi saboda yana iya sadaukar da ita a tsafi don ya samu kuɗi.
Ta ƙara da cewar ta yi yaji a gidan aurenta tun sanda mijinta bai samu nasara a ƙidirinsa na farko ba.
Ta ce a natse tufafin da nayi amfani da su wajen jinin al’adata na sanya su a wani bukiti na musamman a cikin gidanmu da dare, kawai na dawo in wanke kayan bangansu ba.
Azez shi kaɗai ne ke cikin gidan kuma shi kaɗai ke zuwa in da na ajiye kayan kan haka ni tabbata shi ne ya ɗoke su.
“Na duba ko’ina har daji ban gani ba, sai na je na sanarwa mahaifinsa da gargaɗin in bai dawo da kayan ba zan ci masa mutunci. Kan haka ya dawo da kayan wurin da na ajiye su don na wanke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *