Spread the love

Gwamnatin Neja Ta Haramtawa Shareef Adam Gudanar Limanci Da Tafsiri

* Babu Wata Dokar Kasa Da Haramta Min Gudanar Da Harkokin Addini Dan Haka Zan Garzaya Kotu.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Daga M. A Umar, Minna

Gwamnatin Neja ta haramtawa Shareef Sheikh Adam Minna gudanar da jagorancin sallar juma’a da tafsirai a fadin jihar, lamarin da ya biyo bayan zargin malamin da aikewa da sakon bidiyo a kafar sadarwa ta facebook inda aka zarge shi da kama sunayen wasu sahabban manzon Allah yana zagin su.
Hukuncin haramtawa malamin gudanar da duk wani karantawa a jihar ya biyo bayan kafa wani kwamiti karkashin hukumar kula addinai bisa jagorancin Dakta Umar Faruq Abdullahi, inda kwamitin ta gayyaci malamin dan kare kan sa daga zargin da suka ce ya kasa bada hujjoji akan zargin da ake masa.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Gwamnatin jihar ta ba da sanarwa a gidan radiyon jiha da wani radiyon mai zaman kan sa na Prestige, inda ta shelanta haramtawa malamin cigaba da jagorantar sallar juma’a da ya ke yi a masallacin juma’ar As-safinah dake London Street, da kuma gudanar da tafisirai da wa’azozi a dukkanin fadin jihar, inda gwamnatin ta bayyana cewar ta sanar da jami’an tsaro da shugabannin kananan hukumomi ashirin da biyar wannan haramcin.
Sheikh Adam, wanda tsohon mai baiwa tsohon gwamna Dakta Babangida Aliyu shawara ne akan harkokin addini a jihar da yace ya shekara arba’in yana wa’azi a jihar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a gidansa larabar makon nan mai karewa, yace malamai da dama sun san gaskiya amma suna boyewa mabiyan su, domin duk abinda ya faru sun sani amma ba sa fadawa mabiyan su. Yace abinda aka boye a cikin addini a bayyana shi tunda musuluci ba kungiyar asiri ba ne.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Na dade ina wa’azi ba sa so, kuma ba sa iya fuskanta ta, suna ta neman hanyoyin da zasu dakusar da ni Allah bai yarda ba, karatun da na yi ya janyo wannan cecekucen da suke ta kafurta mutane shi ne tsokaci akan karatun wani malami, wanda na nuna kuskuren malamin akan fifita sahabin manzon Allah akan manzon Allah da yazo da addinin nan.
Shehin malamin ya cigaba da cewar ranar talatar nan an kira ni taron zaman lafiya a hukumar kula da harkokin addini ta jiha, bayan na tafi na tarar da dakin taron da malaman addini da jami’an tsaro da yan jarida, sai aka sanya murya ta, bayan nan suka tambaye ni cewar muryata ce na amsa cewar ni ne, sai aka ce malamai su saurara sai ayi hukuncin da ya dace, na tambaya cewar daga zama sai hukunci, ai ya kamata a saurari bangare na, sai suka ce ba a zo wannan bagiren ba.
Kafin wannan zaman akwai malaman da suka kira ni kan in janye maganganu na dan a zauna lafiya, bayan mun yi maganganu kuma na janye, yau sai wannan maganar ta taso, ganin yadda zaman ya dauki zafi aka umurci in fita waje tare da almajirai na, haka kuma mu ka yi. Saboda an ce maganar zaman lafiya kuma da hukuma a ciki dole mu mika wuya dan mun san anfanin zaman lafiyar.
Wadanda ke jagorantar wannan wajen kafin su na zama mai baiwa gwamna shawara akan harkokin addini, na samu lambar yabo da dama akan zaman lafiya a lokacin gwamnatin da ta shude, shi yasa duk abinda suka yi tayi min ban damu ba tunda da sunan gwamnati suke magana, ba irin cin mutunci da zagin ba su yi min ba, amma Allah cikin ikonsa ba mu ce komai ba.
Lokacin da suka baiwa yan jarida damar yi min tambaya, tambayar itace me zan ce game da hukuncin da suka yi min, na ce ban yarda ba dan ba a min adalci ba, da yamma kuma sai mu ka ji radiyo cewar gwamnatin jiha ta dakatar da ni jagorantar sallah da wa’azoza a fadin jihar.
Sheikh Adam ya cigaba cewar ina baiwa gwamnatin jiha shawara da ta zama adila, ba haka ake gwamnati ba, ya kamata ne a ce gwamnati ta gayyaci dukkan bangarora ne mu yi karatu sai tayi nazari ta yanke hukuncin da ya dace, domin za ta iya gane wannan tunda tana da hankali.
Yanzu matsayin mu akan wannan hukuncin na su, za mu hanyoyin da suka dace cikin maslaha daga farko a karshe amma idan ma rigima suke so ba za mu yi ba.
Ba mu sabawa dokokin kasar nan ba, mu ba yan tada zaune tsaye ba ne. Hanyar da dokokin Najeriya tace mu bi wajen kwatar yancin mu, shi za mu bi, amma ba tashin hankali ko rigima ba. Inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *