Spread the love

Ministan kula da jinƙan ɗan adam da ‘yan gudun hijira Sadiya Umar Faruk ta ce sama da miliyan biyu mutanen Nijeriya ke gudun hijira a wasu wurare saboda aiyukkan mahara da ‘yan ta’adda da sauran aiyukkan ɓarna.

Sadiya ta ce abin da ke gaban ma’aikatarta shi ne tabbayar da tallafin ƙasa dana ƙasashen waje matuƙar aka bayar ya isa ga jama’a, a kuma kare ‘yancinsu na zama ‘yan ƙasa.

Ta ce suna iyakar ƙoƙarinsu su tabbatar ‘yan gudun hijira sun samu gudunmuwar da za ta taimaki rayuwarsu, da sake gina matsugunnin da ‘ibtila’i ya ɓarnata domin mutane su koma muhallansu, suna ƙoƙarin ganin cikar burinsu da al’umma za su murna.

Ministar ta yi kalaman ne a ziyarar da masu lalura ta musamman suka kaiwa shugaba Buhari a fadar gwamnatin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *