Spread the love

Ministan shari’a Abubakar Malami ya samu wasu muhimman nasarori guda 20 a shakarar data gabata ta 2020 duk da yanda cutar Korona ta yi wa tattalin arziki shakar mutuwa ta gurgunta harkokin tafiyar da gwamnati da kasuwanci da harkokin yau da kullum.
Duk da hakan a shekarar data gabata ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya ministan shari’a Abubakar Malami ya sadaukar da kansa a wurin yi wa al’umma hidima dokar kullen ba ta hana shi cimma nasarori ba ga guda 20.
Dakta Umar Jibrilu Gwandu mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a na ministan ne ya fitar da bayanin abubuwan guda a 20 in da Managarciya za ta kawo kadan daga cikinsu a wannan karon daga baya za ta kawo wa mai karatu sauran.
Ministan Shari’a ya samar da wata hanya da za ta yaki cin zarafin mata don kawar da shi gaba daya, kan haka ya kafa kwamiti wanda ofishinsa zai dubi duka dokokin ake da su a kasa, da samar da cikakken bayanin wadanda matsalar ta shafa don a yi adalci ba tare da daukar dan mowa da bora ba.
Na biyu minista jajirtacce ne musamman a wajen aiki a shekarar data gabata ya karbi sakoni ta akwatin kafar sadarwarsa(emails) guda 13,772, ba wani sako da bai yi aiki kansa ba tun daga Junairu zuwa Disamban 2020. Ministan ya karbi sakonin ne daga ma’aikatun gwamnati, sakonnin su ne 5281 daga cambobin lauyoyi daban daban da wasu 756 daga kungiyoyin sa kai, sauran 3056 ya karbe su ne daga daidaikun mutane.
Na uku minista shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya shi cikin mambobi kwamitin wutar lantarki a wani kwamiti na musamman da ya kafa kan harkar wutar lantarki a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *