Spread the love

Gwamnan jihar Rivers Nyesome Wike ya ce ‘yan Nijeriya suna tsumayen dawowar jam’iyar PDP saman mulkin Nijeriya domin gudanar da gwamnati mai kyau.
Gwamna Wike ya fadi hakan a lokacin da yak kaddamar da hanya mai tsawon kilomita 11.53 da ta hada kananan hukumomin Eleme da Oyigbo a jihar.
Sanata Muhammad Ali Ndume ne ya kaddamar da bude hanyar, a wurin gwamnan ya ce mutanen kasa na bukatar gwamnati mai kyau da bunkasar tattalin arziki da samar d aiyukkan cigaba, abubuwan da PDP ke yi a jihohin da suke jagoranci.
Ya ce aminta da mutanen kasa suke ga jam’iyar PDP yake kira da Ndume da jam’iyarsa su girmama ra’ayin ‘yan Nijeriya wanda hakan ke tabbatar da dawowar PDP saman mulki a 2023.
Ndume da ya kaddamar da hanyar ya nuna farincikinsa ga damar da aka ba shi na na bude wannan hanyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *