Kakakin majalisar dokokin jihar Sakkwato Honarabul Aminu Muhammad Achida ya baiwa mawaƙi mota a gaban gwamna Aminu Waziri Tambuwal lokacin da yake ƙaddamar da soma aikin magudanun ruwa a unguwar Mabera wanda haɗin guiwa ne tsakanin gwamnatin jiha da bankin duniya.
Mawakin da ke salon waƙar gargajiya ya rera waƙar yabon Tambuwal a ƙarshe ya buge da roƙon Aminu Achida ya ba shi kyautar mota anan take ya aiko ya ba shi, abin da ake ganin ya yi ne domin idon gwamna.
Masu wannan hasashen sun ce ya yi hakan ne domin ya samu shiga a wurin gwamna Tambuwal sun ƙarfafa nazarin ne da hujjar cewa Kakakin ba ya da sunan kyauta a jihar.
Shekararsa sama da ɗaya yana jagorancin majalisa amma ba a ganshi a wurin ƙaddamar da wata gidauniya ta addini ko ta ‘yan nanaye ba, ba a ji shi da bayar da gudunmuwa ga magoya bayan tsohuwar jam’iyarsa da ya kori kansa ba, sai ga shi a gaban Gwamna ya ba da kyautar mota wanda ba shi ne karon farko ba.
“Wannan kyautar tasa buki ne ya mayar kan alherin da gwamna ke yi masa ko kuma yana son karin samun shiga ne ne ya ga bari ya nunawa gwamna shi ma wani zarumi ne da yake iya fitar da kitse wuta in dama ta samu, amma kash sunan kura ya faɗi tun tana ƙarama.” a hasashen masu nazari kenan.

Leave a comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *