Spread the love

Daga Muhammad M. Nasir.

Al’ummar kananan hukumomin Sakkwato ta kudu da ta arewa a jihar Sakkwato na da kishirwar wakilci a majalisar tarayyar Nijeriya musamman a wannan majalisa ta 9.
Jama’ar na bukatar samun mutum gwarzo mai jajircewa da kuma tsayi kai da fata ga bukatun al’ummar da yake wakilci.
Siyasar Nijeriya da jihar Sakkwato ta fara bunkasa in da mai jefa kuri’a ya fara tunanin ya tambayi wanda zai zaba mi ka yi na cigabana kafin na aminta na sa ka gaba ka wakilce ni a sauran lamurran yau da kullum.

Honarabul Sanusi Danfulani yana daya daga cikin mutanen da ke son samun damar su wakilci jama’ar yankin, masu bibiyar lamurran yau da kullum sun tabbatar zai iya wakilci nagari matukar ya samu dama.

A yanzu da Honarabul Sanusi baya wakiltar mutane a kowace majalisa ko gwamnati amma ya tsaya kan bukutunsu da kokarin share hawayensu daidai gwargwadon abin da yake iyawa, har ya sa mutanen da suka ci karo da shi sukan kira shi da MALIYA.

Sanusi Danfulani ba wani bangere na rayuwa da bai bayar da gudunmuwarsa ba domin ganin dai al’umma ta samu cigaba musamman matasa maza da mata, mutum ne da yake yaki da rashin aikin yi a tsakanin al’umma.
Halayyar Honarabul ta girmama mutane da son taimakon duk wani mai basira don ya iya dogaro da kansa, da yanda yake kin maula da bangar siyasa da kai makura ga fada da halin cima kwance a cikin al’umma ya sanya martabarsa da soyayyarsa na kara yawa a tsakanin zukatan jama’a musamman wadanda suka san abin suke yi da ke neman mai wanda yake kokarin kafa al’umma ta gari.

Danfulani yakan yi kyauta da taimako ba don biyan bukatar kansa ba sai don tausayi da nemawa mabukaci mafita, wannan abu ne ya tsarewa tsaransa da shi, matukar mutanen kananan hukumomin nan da yake son ya wakilta suka same shi lalle sun dace da wakili wanda ba zai je domin dumama kujera ba, fata dai ya samu nasara don shayar da al’ummarsa romon dimukuradiyyar da za ta magance masu wannan kishin da ke ci gaba da addabarsu.
Danfulani dan jam’iyar APC ne kuma anan ne zai yi takararsa da yawan magoya bayan jam’iyar PDP suna fadin za su zabe shi matukar ya samu damar tsayawa takara don sun gamsu da yanda yake jan zaren siyasarsa yana yi ne domin jama’a gaba daya bai da fata da ta wuce cigaban Sakkwato da Nijeriya baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *