Spread the love

Zamfara zata gina gidan gyara halin ka guda 4.

Daga Aminu Abdullahi Gusau.

Gwamnatin jihar zamfara tace za ta gina tare da samar da cibiyoyin gyara hali hudu 4 a fadin jihar.

Kwamishinan kananan hukumomi da cigaban al’umah na jihar zamfara Alhaji Yahaya Chado Gora Namaye ya bayyana hakan a lokacin da yake karba bakuncin shugaban gidan hukumar gyara hali ta kasa reshen jihar zamfara Alhaji Sulaiman Isiyaka a offishin sa dake Gusau hedikwatar jihar Zamfara.

Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar zamfara a karkashin jagoranci gwamna Bello Muhammed Matawallen Maradun ,tana fadi tashi waje taimakawa hukumomin gwamnatin tarayya dake aiki a jihar.

Honarabul Yahaya chado ya Kara da cewa a bisa ga wannan ne maigirma gwamna matawalle ya maida hankali wurin samarwa al’umah jihar abubuwan more rayuwa, a cikinsu harda samarda ingantacen tsaro domin ba da kariya ga rayyuka da Kuma dokiyoyin jama’a da ke cikin jihar ta Zamfara.

Ya Kara da cewa gwamnatin gwamna Matawalle a bangaren tsaro ta kubutar da sama da mutum 2000 ga hanuwan masu garkuwa da su da aka dauke lokacin mulkin gwamnatin da ta gabata ta hanyar sulhu da mutanen da su kayi garkuwa da su.

Kwamishinan ya bayyana mahimmancin sulhu da gwamnatin zamfara take yi a halin yanzu inda a cewarsa sa ya haifar da al’fanu,da Kuma cigaba mai ma’ana.

Shi ma ana sa jawabin Babban sakatare a ma’aikatar Alhaji Abubakar Jafar Walin Maradun ya bayyana cewa ma’aikatar zata samar masu da dukanin bukatocin da suka gabatar domin samun cigaban jihar.

Ya ce gwamnati mai ci yanzu tana marhabun lale ga duk wani abu da ya shafi cigaban jihar Zamfara.

Tun farko da yake jawabi shugaban na hukumar gyara hali ta kasa reshen jihar Zamfara Alhaji Sulaiman Isiyaku ya bayyana gwamnatin a matsayin mai son kawo cigaba da kuma kokari wajen samar da ingantacen zaman lafiya da tsaro ta hanyar sulhu.

Shugaban a don haka ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta ba su cikkaken goyon baya domin su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata ta hanyar taimaka masu da bude offisoshi 4 na gyara hali a hedikwatocin kananan hukumomin, Maru,Talata Mafara, Gummi,Kaura Namoda,da Kuma Gusau.

Ya Kuma godewa kwamishinan da dukanin ma’aikatan shi a bisa tarbon da Kuma karamchin da suka nuna masu.

Ya bada tabbacin cigaba da ba da hadin Kai da goyon baya domin ciyar da jihar Zamfara gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *