Spread the love

Ba Zamu Lamunci Duk Yunkurin Rusa Shirin Inganta Makiyayar Zamani Ta Bobi Ba

M. A. Umar, Minna.

Gwamnatin Neja ta bayyana cewar ba za ta lamunci duk wani yunkurin rusa shirin makiyayar zamani ( Bobi Grazing Reserve) da ta kashe miliyoyin naira dan inganta shi ba, makiyayar wanda ke tsakanin kananan hukumomin Mariga da Mashegu a jihar Neja.
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci wajen littinin din makon nan, inda ya bayyana cewar yawaitar karuwar garkuwa da mutane da satar shanu, da hare-haren da mahara ke kaiwa jama’a a wasu sassan jihar, yace gwamnatin jiha za ta dauki dukkan matakan da su ka dace wajen tsare wajen.
Yace gwamnatin jiha ba za ta bar kowace irin kafa da maharan da masu garkuwa da jama’a zasu gurgunta makiyayar wadda ke da hekta dubu talatin da hudu da aka samar da abubuwan more rayuwa.
” Ba tare da bata lokaci ba, ina iya tabbatar da cewar mun tsayu akan wannan shirin za mu tabbatar mun samar da ingantaccen tsaro dan tsare dukiyar jama’a da suka zuba jari a wannan wajen.”
Gwamna Sani Bello, ya jawo hankalin Fulani mazauna yankin da su zauna lafiya, wanda zai ba su damar shiga shirin inganta ruga dan karuwar tattalin arziki da cigaban jihar.
Gwamnan ya jawo hankalin mazauna yankin musamman Fulani da su zama masu sanya idanu dan bada tsaro abubuwan cigaba na more rayuwa da aka zuba a makiyayar, kar su cigaba da baiwa baki matsugunni ba bisa ka’ida ba dan kaucewa baiwa mugu damar samun mafaka yana cutar da jama’a.
Da yake bayani, shugaban Fulani mazauna yankin, Malam Ardo Abubakar ya bayyana cewar aikin makiyayar na samun nasara.
” Mun shaida irin cigaban da ake samu dan mun yi shuka kuma mun girbe, mun ga irin alherin da muka samu sakamakon bude wannan wajen, an lurar da mu irin alherin da ke wannan wajen za mu sanya idanu sosai dan ganin cigaban wannan makiyayar dan mu ne za mu anfana.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *